Gwamna Uba Sani ya tsaya tsayin daka wajen ceto mutane 58 da aka yi garkuwa da su a Kaduna
Akalla mutane 58 ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
An sake su ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba, 2024, ta hanyar tsari masalaha da gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, tare da hadin gwiwar ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) suka gudanar.
Wannan wani gagarumin aiki ne, musamman idan aka yi la’akari da yawaitar sace-sacen mutane a yankin.
Babban kwamandan runduna Manjo Janar Mayirenso Saraso, shi ne ya jagoranci aikin ceton hadin guiwa, inda ya nuna yadda Gwamna Sani ya jajirce wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar Kaduna ta hanyar amfani da hanyoyin masalaha a tare da hadin gwiwar jami’an tsaro.
Bayan an sako su, an kai wadanda aka ceto galibi yara da mata zuwa ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu domin tattaunawa bayan an duba lafiyarsu.
Daga baya an mika su ga babban hafsan hafsoshin Najeriya Janar Christopher Musa wanda shi kuma ya mika su ga gwamna Uba Sani wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa Sani Kila.
A wata hira da manema labarai, shugaban ma’aikatan gwamnan jihar, Sani Kila, ya godewa shugaban kasa Bola Tinubu, NSA da sojoji bisa goyon bayan da suka bayar da kuma kokarin da suke yi na magance matsalar rashin tsaro a Kaduna da shiyyar Arewa maso Yamma.
Ya ce: “Ina so kawai in gode wa shugaban kasa kuma kwamandan rundunar sojojin Najeriya, Bola Tinubu, NSA, da dukkan hukumomin tsaro da ma gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani. A gaskiya ya cancanci yabo domin ya yi kokari sosai wajen ganin an sako wadanda lamarin ya shafa.
Ina kuma so in gode wa malaman addini da na gargajiya saboda goyon bayan da suke bayarwa, domin tsaro aikin kowanne hali Mu hada kai mu yaki wannan rashin tsaro”.
Da yake mika wadanda aka ceto ga wakilin Gwamna Uba Sani, babban hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa, ya ce wadanda harin ya rutsa da su sun samu raunuka kuma bayan an sallame su.
“Shida daga cikinsu suna da ciwo mai tsanani kuma an yi musu magani. An ba su abinci mai kyau, an yi musu sutura da kyau kafin a gabatar da su a nan Don haka Muna mika godiya Gwamna inji shi.