Labarai

Gwamna Uba Sani ya yi maraba da sako ragowar daliban makaranta wanda ‘yan bindiga suka sace tun a shekara ta 2021

Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi maraba da sako dalibin karshe na makarantar sakandare ta Bethel Baptist, Treasure Ayuba, wanda yana cikin wadanda aka sace a shekarar 2021.

Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro a duk makarantun jihar.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a cikin wata sanarwa a Kaduna ranar Asabar ta hannun babban sakataren yada labaran sa, Muhammad Shehu.

“Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya bayyana farin cikinsa da sakin Treasure Ayuba, dalibi na karshe da aka yi garkuwa da shi a makarantar sakandare ta Bethel Baptist, wanda ake garkuwa da shi tun shekarar 2021,” in ji Mista Shehu.

Gwamnan ya yaba da kokarin makarantar da sauran mutane wajen ganin an sako daliban.

“Dalibin da aka sako yana cikin yara 121 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a watan Yulin 2021 daga harabar makarantarsu da ke Maraban Damishi, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna,” in ji shi.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button