Tsaro

Gwamna Wike zai bada tukwicin naira Miliyan Hamsim (50m) ga duk wanda ya nuna maboyar shugaban IPOB Stanley Mgbere wanda ya Jagoranci zanga-zangar da ta jawo kone Kone don gabatar dashi a kotu.

Spread the love

Gwamnatin Jihar Ribas, Zata Bada Tukuicin Miliyan 50, ga duk Wanda ya Fadi Inda Shugaban IPOB yake…

Gwamnan Jihar Rivers a kudancin Kasar nan ya jaddada haramta ƙungiyar,- Indigenous Peoples of Biafra (IPOB) a jihar, wadda ke fafutikar neman kafa ƙkasar Biafra daga Najeriya.

A watan Satumban 2019 ne Shugaba Buhari ya saka hannu kan wani umarnin gwamnati da ya haramta ƙungiyar da ayyukanta a ƙasa baki daya.

Gwamna Nyesom Wike, wanda ya bayyana haka cikin wani jawabi da ya yi wa jama’ar jihar a daren Jiya Juma’a, ya ce daga yanzu an haramta dukkanin wata zanga-zanga da ƙungiyar za ta gudanar a faɗin jihar.

Gwamnan ya ayyana Stanley Mgbere a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa jagorantar zanga-zangar da ta haddasa tashin hankali da lalata dunkiya a Ƙkaramar Hukumar Oyigbo ta jihar.

Kazalika, Wike ya ce zai bayar da naira miliyan 50 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama Stanley Mgbere da gurfanar da shi a gaban kotu.

“An umarci jami’an tsaro da su dakile duk wata zanga-zangar IPOB a Jihar Rivers ko wani ɓangare na jihar tare da kama duk wanda ya bayyana kansa a matsayin ɗan ƙkungiyar,” a cewar wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen yaɗa labarai ya fitar.

Sanarwar ta ƙkara da cewa gwamnati za ta yi dokar da za ta jaddada haramcin ƙkungiyar a Fadin Jihar.

Ko a zanga zangar nan ta #EndSars da aka Gudanar Kwanan nan ‘yan Kungiyar Sun Kashe Hausawa mazauna Yankun su da dama da kuma lalata Dukiyarsu bisa Umarnin Nnamdi Kanu.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button