Lafiya

Gwamna Ya Kamu Da Corona Virus.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Gwamnan Jahar Ondo dake Kudu maso Yammacin Kasar Nan Rotimi Akeredolu Ya Kamu da Cutar Numfashi Ta Covid-19.

Akeredolu din ne Ya Baiyana Hakan a Shafinsa Na Twitter a Yau Talata, Yace Zai Killace Kansa Har Zuwa Wani lokaci Sai dai Yace Zaici gaba da Gudanar da Aikinsa Na Gwamna daga Inda Ya Killace Kansa.

Gwamnan Ya nemi Mutane su yi masa Addu’ar Samun Lafiya.

Wannan dai shi ne Gwamna Na 5 da Suka taba Kamuwa da Cutar a Cikin Gwamnonin Kasar Nan.

Gwamnonin da suka taba kamuwa da Cutar Sunhada da:- Abia, Bauchi, Kaduna, Oyo da Na Ondo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button