Labarai

Gwamna Zullum ya gabatar da kasafin kudin Shekarar 2021 Bilyan N208.7

Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Laraba, ya gabatar da kasafin kudi har N208.7 biliyan na shekarar 2021 ga majalisar dokokin jihar don amincewa da shi.

Farfesa Zulum, Lokacin da yake magana yayin gabatarwa a Maiduguri, ya ce kasafin kudin, wanda aka yiwa lakabi da “Kasafin Kudin Jama’a, Maidowa da Sulhu,” ya kai kusan kashi 15.2 bisa dari (N62.04 biliyan) sama da na shekarar 2020.

Zulum ya yi bayanin cewa Ma’aikatar sake ginawa da sake tsugunar da Yan Gudun Hijira ita ce ke da kaso mafi tsoka da N15.84billion, yayin da Ma’aikatar lafiya ita ce ta biyu mafi girma da ta ware naira biliyan 10.

Ya bayyana cewa, babban kudin da aka kashe ya samu kaso mafi tsoka na Naira biliyan 135 yayin da kuma kudaden da aka maimaita ya kai Naira biliyan 72.

Ya kara da cewa kudurin dokar kasafin kudin na 2021 za a samu kudaden ne daga kason tarayya, abokan hadin gwiwa, kungiyoyin bada tallafi da kuma kudaden shiga da ake samu a cikin gida.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button