Tsaro

Gwamna Zulum Ya Ce Akwai Lauje Cikin Nadi Game Da Yakin Da Akeyi Da Boko Haram.

Spread the love

Gwamna Zulum ya ce ƙoƙarin murƙushe ƙungiyar Boko Haram na shan zagon ƙasa daga wani rukuni na jami’an tsaro.

Babagana Umara Zulum ya ce ba zai iya yin shiru cikin yanayi na kashe-kashe ba, saboda rantsuwar da ya yi tsakaninsa da Allah a kan zai kare al’ummar jiharsa.

Wannan na zuwa ne yayin da jihar Borno ke ganin ƙaruwar hare-haren ‘yan ta’adda.

Ko a ranar Asabar ma sai da wani hari ya kashe mutum 15 ciki har da ƙananan yara a yankin kan iyaka Najeriya da Kamaru.

Gwamnan Zulum ya ce akwai buƙatar shugaba Muhammadu Buhari ya san cewa zagon ƙasan da ake yi daga cikin harkar tafi da tsaro na kawo cikas ga ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin ‘yan ta’addan na sama da shekara goma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button