Labarai

Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Kwamitoci Biyu Domin Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijirar Marte, Ngoshe Da Kirawa.

Spread the love

A yau ne gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umar Zulum ya kafa kwamitocin da za su yi aikin kwashe bakin hauren da ke jihar ta Borno.

A cewar rahoton, Farfesa Babagana Umara Zulum a yau ya kaddamar da kwamiti biyu masu karfi don jagorantar shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar daga Marte, Ngoshe da Kirawa.

Kwamitocin biyu daban daban karkashin jagorancin Hon. Ahmad Babayo Memba mai wakiltar Chibok, Damboa da Gwoza don jagorantar sauya matsugunan Ngoshe da kirawa da Hon. Mustapha Gubio Kwamishinan RRR na yanzu da zai jagoranci kwamitin sake tsugunnar da ‘yan gudun hijirar Marte.

A jawabinsa na rantsarwa, Gwamna Zulum da farko ya yi godiya da yabawa kwamitin na Baga bisa wannan aiki da suka yi, don haka yanzu ya umarci kwamitocin da su yi iya kokarinsu don ganin yadda ‘yan gudun hijirar suka koma gidajensu.

Ya kara da cewa, kwamitin zai yi aiki kafada da kafada da Sojoji da sauran jami’an tsaro don sauya matsugunin.

Wannan ko shakka babu babban labari ne mai kyau ga mazauna jihar Borno wadanda rikice-rikice suka addabi jihar tsawon shekaru.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button