Labarai

Gwamna Zulum ya koma garin Dikwa bayan hari na biyu, ya yi Sallar Juma’a a garin, ya cewa mazauna garin Buhari ya ba da tabbacin samar musu da tsaro.

Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Juma’a ya koma Dikwa don ganawa da ‘yan kasa tare da tantance irin barnar da harin Boko Haram yayi na ranar Litinin a garin.

Zulum ya ga irin ta’addancin da maharan suka yi a fadar Shehu na Dikwa, da hedkwatar sojojin Najeriya ta 81 DIV TF BN NASC 9 Hedikwatar, 22 Armored Brigade Headquarter, UN Humanitarian Hub, Primary Healthcare Centre da IDP sansanoni.

Gwamnan ya kuma umarci Ma’aikatar sake ginawa, Gyaran wurin zama da sake tsugunar da ‘yan gudun hijira da ta gyara duk wasu kadarorin da aka lalata, gami da na sojoji.

Ya jajantawa dangin da harin ya shafa, sannan ya umarci dukkan mazauna yankin da su ba jami’an tsaro hadin kai ta hanyar kai rahoton motsin da ba sa tsammani a kowane lokaci.

Bayan ya kasance tare da mazauna yankin don yin sallar juma’a, Zulum ya isar da tabbacin Shugaba Muhammadu Buhari ga mutane.
“Na yi ganawa da Mista Shugaban kasa a ranar Talata, ya ba ni tabbaci cewa ana daukar matakai don tabbatar da zaman lafiyarku. Ina kira gare ku da ku yi haƙuri da juriya, muna sane da mawuyacin halin da kuka samu kanku kuma muna tare da ku, ba hutawa muke yi ba. Muna yin duk abin da za mu iya kuma insha Allah, za mu cimma burinmu ”in ji Zulum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button