Gwamna Zulum Ya Tallafawa Iyalan Marigayi Hazikin Soja Kanar Bako Da Zun-zurutun Kudi Har Naira Miliyan 20 ..
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana mutuwar marigayi Kanar. Bako a matsayin wani lokaci mai cike da bakin ciki ga dangin mamacin, sojojin Najeriya da kuma mutanen jihar Borno da ma kasa baki daya.
Zulum ya bayyana marigayi Kanar Bako a matsayin hazikin gwarzo kuma kwararren jami’i wanda a karkashin jagorancinsa Damboa ta sami ‘yanci daga ‘yan ta’addan Boko Haram.
A cewarsa, Marigayi Kwamandan ya kasance mai jajircewa, taka tsan-tsan da jajircewa wajen sauke nauyin da aka dora masa, kuma ya ba da gudummawa matuka wajen yaki da tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas.
Ya ce: “Shima yana daya daga cikin abubuwan da suka tabbatar da kiyaye jihar Borno a wannan lokaci na tayar da kayar baya, ba Borno kadai ba har ma da jihar Yobe.
“Za mu tuna da shi har abada saboda irin gudummawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya a Jihohin Borno da Yobe da ma kasar baki daya.”
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya saka masa da Aljana firdaus tare da sauran jami’ai da kuma mutanen da suka rasa rayukansu a yayin sauke ayyukansu.
Ya kuma sanar da cewa Gwamnatin Jihar Borno za ta samar da gidan da ya dace ga dangin jami’in da ya mutu don tabbatar musu da kwanciyar hankali.
Ya kuma ba da gudummawar Naira miliyan 20 don tallafawa bukatun jin daɗin iyalan mamacin.
Zulum ya ce: “Ina sane da cewa Sojojin Nijeriya suna bayar da tallafin karatu ga’ ya’yansa sannan kuma za mu ba da goyon baya don tallafawa kokarin sojojin Najeriya.
“Don jin dadin danginsa, Gwamnatin Borno za ta fitar da Naira miliyan 20 kuma za a mika ga danginsa kwanan nan ko gobe da safe.
“A wannan lokacin, bari na sake mika godiya ta ga sojojin Najeriya.” Shugaban hafsin sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, yayin jana’izar marigayin, ya bayyana shi a matsayin haziki kuma maras tsoro wanda za a ci gaba da tunawa da sadaukarwar da ya yi.
Buratai ya bayyana cewa marigayi Kwamandan ya kasance mai kwazo wajen yaki da masu tayar da kayar baya daga bangarori daban-daban a filin daga na Arewa maso Gabas.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa matar marigayi kwamandan, wacce ta samu rauni bayan mutuwar mijinta, tana karbar magani a asibitin sojoji da ke Maiduguri.