Al'adu
Gwamna Zulum Ya Ziyarci Iyalan Sojan Da Fashewar Bom Ta Ritsa Dashi.
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Gidan Sojan da Bam Ya Kashe a Wajen Aikinsa a Borno.
Sojan Marigayi Laftanar. Babakaka Shehu Ngorji, Ya Hadu da Ajalinsa ne Lokacinda Bam Ya Fashe a Costom da Kulogumna dake Arewacin Maiduguri.
Zulum Ya Jajantawa Iyalan Mamacin a Maiduguri, Kana ya Ambaci Ngorji da Jarimi mai Kishin Kasa da Jahar sa. Sannan Yayi masa Addu’ar Allah Yasa Aljannace Makomarsa.
Ahmed T. Adam Bagas