Labarai
Gwamnan Borno ya Karbi bakuncin Shugaban ICRC a birnin Maiduguri.
Gwamnan Jahar Borno, Babagana Umara Zulum a Yau Talata ya karbi Kwamitin Kungiyar bayar da agajin gaggawa ta ICRC ta kasa da kasa na Majalisar Dinkin Duniya Markus Dolder a Gidan Gwamnati dake Maiduguri.
Taron wanda aka gudanar an tattauna batun da ya shafi ci gaban jahar Borno, wanda ya ta’allaka kan batun bayar da sabis na kiwon lafiya, samar da ruwan sha da matsuguni ga al’ummar Jahar da ke zaman gudun hijira a Jahar.
Kungiyar agaji ta ICRC tana tallafawa gwamnati wajen biyan bukatu da jin dadi tare da bayar da tallafin kula da lafiya ga yan gudun hijirar a jahar Borno.