Tsaro
Gwamnan Borno Ya Ziyarci Garin Da ‘Yan Boko Haram Suka kashe Mutane 81 a Jahar.
Gwamnan Jahar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Faduma dake karamar Hukukumar Gubio ta Jahar Borno.
Garin Faduma dai nan ne Mayakan Boko Haram suka Kashe mutane 81 Har lahira a Daren Shekaran jiya Litinin.
Zulum Yakai ziyarar gani da ido ya Jajantawa Al’ummar da Bala’in Ya shafa.
Allah ya kawo mana Dauki kan wannan Bala’in….
Daga Ahmed T. Adam Bagas