Rahotanni
Gwamnan Borno Yaki Amincewa Da Inagancin Bulon Gina Gidaje 500 a Auno.

Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnan Jahar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum Yaki Amincewa da Ingancin Bulon da za’agina Rukunin Gidaje Dari biyar da ya bada Umarnin Ginawa a Garin Auno dake karamar Hukumar Konduga ta Jahar Borno.

Zulum yaje Rangadin Ganin Aikin ne a Auno yace a Canza Bulon da ake Aikin kasancewar Bashi da Karfi yana Fashewa.
Rangadin Zulumdin Bai Tsaya Auno Ba yaje Ganin aikin Gina Gidajen Saukar baki da Ya bada Umarnin ginawa Na Jami’ar Borno da Gina Makarantar Sakandren Momari.
Gwamnan yayi Ziyarar Rangadin ne Yau Asabar bayan Dawowarsa Daga Abuja Inda Ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan Sha’anin Noma a Jahar Ta Borno.
