Addini

Gwamnan Ganduje Ya Goyi Bayan Hukuncin Kisa Ga Wanda Yayi Batanci Ga Annabi.

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya goyi bayan hukuncin kisa, da aka zartarwa Mawakin nan, Wanda aka samu da lefin yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam.

A makwannin baya ne wata Babbabr kotun Shari’a’r Musulunci ta zartar da Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya ga Mawaki Sharif mazaunin unguwar Sharifai dake nan jihar Kano, sakamakon samunshi da lefin yin batanci ga fiyayyen Halitta Annabin Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam, Wa ‘iyazubillah.

Gwamnan yace da an kammala dukkanin abubuwan da Shari’a ta gindaya na daukaka kara zuwa kotun koli ko akasin haka zai sanya hannu Dan aiwatar da hukuncin kisan.

Sakataren yada labaran gwamnan Jihar Abba Anwar shine ya tabbar da haka cikin wata sanarwa da aka fitar da almurun wannan Rana.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button