Gwamnan Jihar Diffa, Dake Jamhuriyar Nijar Mai Makobtaka Da Jihar Borno Ya Jinjinawa Gwamna Zulum.
Gwamna Jihar Diffa Alhaji Isa Lameen, ya kasance a birnin Maiduguri ne don jajantawa Farfesa Babagana Umara Zulum, kan harin da aka kaiwa ayarin motocinsa kusa da Baga a farkon wannan watan.
Gwamna Lameen, ya samu rakiyar mambobin majalisar Jihar Diffa, Sakataren gwamnatin ta Diffa, Alh. Yahaya Godi, babban jami’in yan sandan Jihar Diffa, Col. Daye Mohammed, da sauran jami’an shi, da kuma sarakunan gargajiya daga Jihar ta Diffa.
“Gwamnan Diffa, yace mun zo nan ne domin kara karfafa maka guiwa game da abubuwan da dama can kana yi, muna bin diddigin duk wasu ayyuka da kake yi a jihar Borno da Lardin mu na Diffa, mun baka cikakken goyon baya ‘dari bisa ‘dari ga gwamnatin ka.”
Gwamnan Diffa, Ya kara da cewa, Tun lokacin da ka zama Gwamnan jihar Borno, mun sani, kuma muna ganin abubuwan da kake yi. Muna godiya a gareka kuma nuna Fatan za ka cigaba da abubuwan da kake yi na alheri. A Jamhuriyar Nijar, musamman a Diffa, muna rokonka, ka ci gaba da abin da kake yi ga al’ummar ka.”
Gwamna Lameen, ya kara bayyana cewa Borno da Diffa, suna da matsala iri guda na ayyukan yan ta’adda, wanda na yi imanin cewa za a shawo kan matsalar ba tare da bata lokaci ba. Inda ya sake jaddada goyon baya da karfafa guiwa ga gwamna Zulum da jama’ar jahar Borno.
“Dukkanin mu biyu muna da matsaloli iri guda, muna kara ƙkarfafa maka giuwa ka ci gaba da yadda kake domin shawo kan wannan matsala. Ina kuma son kara karfafa irin wannan ziyarar a tsakanin mu, domin muyi nasara akan abokan gaban mu, Da yardar Allah za muci nasara akan makiya mu. Zamu dawo mu cigaba da rayuwar mu ta yau da kullum kamar da, mutanen mu za su samu zaman lafiya harda wadanda suke kan iyakoki. Na yi imanin cewa kowacce matsala tana da iyaka, kuma ƙkarshen maƙkiyan mu zai zo ba da jimawa ba. In ji Gwamna Lameen.
Da yake mayar da jawabi, Gwamna Zulum ya nuna farin cikin shi da ziyarar.
“Zulum yace a madadin gwamnati da jama’ar jihar Borno ina maraba da ku. Tabbas, daukacin jama’ar Borno suna farin cikin ganinku a wannan rana. In ji Zulum.
Gwamna Zulum ya bayyana alakar da ke tsakanin jihohin biyu a matsayin wani muhimmin abu bisa la’akari da kamanceceniyar al’adu, addini da k dangantakar aure, Gwamna ya yi alkawarin ci gaba da kyakkyawar alaka da Su.
Gwamna Zulum ya kuma yabawa Gwamnatin Jamhuriyar Nijar da ta Diffa saboda ci gaba da tallafawa ‘yan jihar Borno da ke neman mafaka a yankin Diffa.
“Zanyi amfani da wannan damar don isar da godiya ga Gwamnatin Nijer da ta jihar Diffa saboda yadda suka kula da ‘yan gudun hijirar mu yadda ya kamata. Insha Allah, za mu tattauna yadda za mu iya dawo da wasu daga cikin mutanen mu wadanda ke shirye su dawo gida cikin. Muna sane da kalubalen tattalin arziki da duniya ke fuskanta, amma duk da haka zamu ci gaba da tallafa wa mutanen mu, hakika muna matukar godiya a gare ku. ” In ji Gwamna Zulum.
Sunci cigaba da ganawar cikin sirri, inda suka maida hankali kan matsalolin tsaro da suka shafi jahohin biyu.
Ahmed T. Adam Bagas