Labarai

Gwamnan Jihar Neja ya Jajantawa Al’ummar Kagara da da ‘yan Bindiga suka kai hari Jiya.

Spread the love

Gwamnatin jihar Neja ta yi kira ga mazauna garin Kagara da ke karamar hukumar Rafi ta jihar da su kwantar da hankulansu, domin gwamnati na tura kayan aiki don tabbatar da kare rayukansu da dukiyoyinsu Inji Gwamnan.

Wannan roko yana zuwa ne a kan yanayin yadda ‘yan fashi suka kai wa garin hari tare da firgicin da wani bidiyo na soshiyal midiya ya nuna, in da aka ga mazauna yankin suna guduwa a matsayin masu neman taimako, kuma suna kiran gwamnatin jihar da sojoji da su shiga Lamarin domin daukar matakan da suka dace.

A cikin sakon ta’aziyyarsa, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ci gaba da cewa babu wata gwamnatin da zata sanya ido ‘yan ta’adda suna zubda jinin al’ummarta masu bin doka da oda.

Gwamnan ya yarda da yawan kalubalen tsaro da ke addabar jihar amma ya tabbatar wa mutane cewa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar shugaban kasa Muhammadu Buhari da jami’an tsaro sun damu matuka a yakin da take yi da kananan kungiyoyin da ke jefa rayuwar jama’a cikin kunci.

Gwamnan ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin tare da yin addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Ya nemi hadin kan mutane don samun bayanai masu amfani ga jami’an tsaro, yana mai tabbatar masu da cewa za a ci gaba da daukar bayanan su domin Inganta Tsaro a yankin.

Harin dai da ‘Yan Fashin suka kai Da yammacin Jiya Laraba a garin Kagara dake karamar Hukumar Rafi da garin Dukku ta karamar hukumar Rijau, yayi Sanadiyyar mutuwar ‘Yan banga 18 da ‘Yan Sanda 3.

Kuma ‘Yan bindigar sun shiga Wata kasuwa a karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Inda suka sace Mutane sama da Ashirin a kasuwar.

Wannan Fitina Allah ya Kawo Mana Dauki.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button