Gwamnan jihar sokoto ya tsige hakimai 15 kan Zargin rashin biyayya ga Gwamnati.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya tsige hakimai 15 daga karagar mulki, bisa zarginsu da laifin rashin biyayya ga Gwamnati, satar filaye, taimakawa rashin tsaro da kuma mayar da kadarorin gwamnati Izuwa gare su.
Sakataren yada labarai na Gwamna Abubakar Bawa ne ya sanar da tsige su da yammacin ranar Talata a cikin wata sanarwa
Hakiman da aka tsige sun hada da: Unguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, lllela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da gundumar Giyawa.
Sauran su ne wadanda tsohon Gwamna Aminu Tambuwal ya nada a karshen gwamnatin sa.
“An soke su ne saboda yanayin nadin da aka yi musu wanda a cewar sanarwar an yi su ne cikin gaugawa da kuma kin amincewa da mutanensu.
Wanda suka hada da Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun Yar Tsakkuwa, Sarkin Tambuwal da Sarkin Yamman Torankavwa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ce an ba da Umarnin cigaba da Shari’o’in da suka shafi Hakiman Isa, Kuchi, Kilgori da Gagi don ci gaba da bincike.
Haka kuma Sarkin Yakin Binji babban mai ba da shawara a Majalisar Sarkin Musulmi aka mayar da shi Bunkari yayin da Hakimin Sabon Birni aka tura Gatawa.
Bawa ya kuma bayyana cewa, gwamnatin ta tsare wasu hakimai bakwai.