Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sha alwashin kawo karshen ayyukan ta’addanci a Jihar Zamfara
Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da ya ziyarci sansanin horar da jami’an tsaro na Community Protection Guards (CPG), wani shiri na gwamnatin sa na yaki da ‘yan fashi a jihar.
Ya kuma bayyana kwarin guiwar yaki da rashin tsaro, inda ya jaddada wajibcin daukar nauyin hadin kai na tabbatar da zaman lafiya.
Na zo ne a yau don shaida yadda ake ci gaba da samun horon da aka dauka na ‘Community Protection Guards’ (CPG),” inji gwamnan a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Sulaiman Bala Idris ya fitar.
“Ina kira gare ku duka (masu daukar ma’aikata) da ku sadaukar da kanku wajen horaswa domin aikin da ke gaban ku yana da girma kuma yana bukatar sadaukarwa ga kasa uwa. Dole ne mu taru don samun sakamako mai inganci. Wata rana zamu shawo kan matsalolin tsaro da muke fuskanta a fadin jihar Zamfara.
“Na yi farin ciki da abin da na gani a sansanin horo. Hakan ya kara sa raina, kuma ina da yakinin cewa aikin cetonmu yana kan hanya, domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga Zamfara.”
Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga. Sauran jihohin sun hada da Kaduna, Sokoto, Katsina da Kebbi.
Duk da kokarin da gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro ke yi na magance matsalar ‘yan fashin, ‘yan bindigar na ci gaba da yin barna a yankin.