Labarai

Gwamnan Katsina Ya Kashe N233m Akan Kula Da Kayan Tsaro A Gidan Gwamnati Cikin Wata Daya.

Spread the love

Duk Da Kashe-kashen Da ‘Yan Bindiga Suke Yi A cewar rahoton SaharaReporters, an cire kudin daga asusun jami’an tsaron jihar a watan Agustan 2018.

Yayin da jihar Katsina ke ci gaba da fada da rashin tsaro, gwamnatin da Gwamna Aminu Masari ke jagoranta ta kashe sama da N233m wajen kula da kayan tsaro a gidan Gwamnati.

A cewar wasu takardun da Jaridar SaharaReporters ta wallafa, an cire kudin daga asusun ajiyar jami’an tsaron jihar a watan Agustan 2018.

“An umurce ni da in isar da amincewa don sakin (N233,000,000: 00) kawai ga Sakataren Gwamnatin Jiha wanda za a biya a matsayin alawus ga jami’an tsaro da kuma kula da kayan tsaro a gidan Gwamnati.

“Kuri’ar cajin kudi asusun tsaro ne,” wasikar da wani Jami’i Bature Danlami ya aike wa babban Akanta-janar na jihar.

Al’ummar Jihar Katsina sun ga yadda ake ta samun karuwar ayyukan ‘yan fashi a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Yawancin al’ummomin jihar sun shaida ana samun karuwar jerin hare-hare daga ‘yan fashi, wadanda suka kware a harkar sata, fashi, jikkata jama’a, kisa da kuma satar dabbobi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button