Labarai

Gwamnan Mai mala Ya Angwance da Gumsu Abacha amatsayin mata ta Hudu.

Spread the love

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban rikon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Mai Mala Buni, ya auri matar sa ta hudu a asirce a wani bikin sirri da aka yi a Abuja.

SaharaReporters ta tattara cewa sabuwar amaryar gwamnan ita ce Gumsu Abacha, daya daga cikin ‘ya’yan tsohon Shugaban kasa na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha.

An ɗaura auren a gidan Mohammed Abacha da ke Abuja a ƙarshen mako.

Wani mai taimaka wa gwamnan ya ce an gudanar da taron ne a asirce don kaucewa sukar jama’a.

Gumsu, mai shekaru 45, a baya ta auri wani hamshakin mai kudin nan na Kamaru, Bayero Fadil Mohamadou.

A shekarar 2019, gwamnan ya auri diyar da ta gada, Adama Ibrahim Gaidam, kimanin awanni 24 bayan rantsar da shi ofis.
Ummi Adama Gaidam, wacce ke karatu a Saudiyya a lokacin, ta yi aure a matsayin matar sa ta uku.

Buni ya kasance Sakataren Jam’iyyar APC na kasa lokacin da Gaidam ya bayyana sha’awar sa a matsayin wanda zai gaje shi.

Kamar yadda yake tare da aurensa da Ummi Adama, diyar magabacinsa, Ibrahim Gaidam, ance aurensa da Gumsu ma anyi shi ne saboda dalilai na siyasa.

Gumsu, diya ta biyu ga marigayi tsohon Shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawan soja, Abacha, da Mohamadou sun rabu a shekarar 2020.

Sun yi aure kimanin shekaru 20 su rabu da Mijin ta, kuma a yanzu ta sami sabon gida a gidan Buni.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button