Siyasa

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal Ya Fara Tuntubar Manyan Najeriya Kan Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2023

Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya fara zagaye wajan masu fada aji a kasarnan inda yake neman shawararsu kan tsayawa takarar shugaban kasa da yake son yi a shekarar 2023.

Tambuwal ya gana da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo inda bayan ganawar me magana da yawun Obasanjon ya bayyana cewa shawara ce kawai wanda ta shafi sha’anin mulki Tambuwal ya je nema wajan Obasanjon.
Munsamo muku daga Rahoton Thisday cewa Tambuwal shawarar tsayawa takarar shugaban kasa ya je yi wajan Obasanjo.

Hakanan Tambuwal din ya nemi irin wannan shawara a wajan Theophilus Danjuma da David Mark.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button