Gwamnan Sokoto Ya Yafewa Fursunoni 17 ya Basu Dubu 50 kowanne.
Gwamnan Jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Afuwa ga fursunoni goma sha bakwai, sannan ya basu tallafin naira Dubu hamsin kowanne mutum daya, da zummar su kama Sana’a.
Ya ce fursunoni uku daga cikin 17 an tsaresu ne da laifuffukan tarayya, yayin da ragowar kuma an tsare sune bisa laifukan jihar.
A NASA jawabin, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan jihar, Suleiman Usman, SAN, yace
Yin afuwar yayi dai dai da doka, gwamnana ya yafewa fursunoni kamar yadda Tsarin dokar kasa ta 1999 ta tanada Inji Shi.
”Wannan karimcin an shirya shi ne domin baiwa tsoffin fursunoni damar sake haduwa da danginsu tare da zama ‘yan kasa nagari.
Ya yi kira ga fursunonin da aka yafe dasu da su nisanci ayyukan mugunta kuma su shiga ayyukan da zasu inganta yanayin rayuwarsu.
Ya ce: “An gudanar da wannan aikin ne ta hanyoyin da suka dace ga fursunoni don yi musu jinkai.”
Ya ce babban lauyan ya kuma gabatar da taimakon kudi naira dubu hamsin N50,000 ga kowane ɗayan da aka yafewa daga hannun gwamnatin jihar yayin yafe musu.
Mista Bello ya lura cewa kudin shine zai basu damar kama sana’a da zasu dogara da kansu, bayan komawa cikin iyalansu.
Mai magana da yawun gwamnan ya yi bayanin cewa Babban Jami’in kula da ayyukan gyara, hali, wanda Mataimakin Shugaban Kula da Gidan yari ya wakilta, Idris Muhammad, ya godewa gwamnatin jihar bisa ci gaba da goyon baya da karfafa gwiwa ga gidan yarin.
Ahmed T. Adam Bagas