Gwamnatin Amurika ta bukaci Gwamnatin Buhari da Takawo karshen Zubda Jini a Arewacin Kasar Nan.

Ahmed T. Adam Bagas
Ma’aikatar Harkokin wajen Amurika tayi kira ga Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari da ya kawo karshen Kashe kashen da Yazama tamkar Ruwan dare ne a Arewa cin Kasar.
A sanarwar da ma’aikatar ta fitar tace Kungiyar dake Kokarin kafa daular Islama a Yammacin Afrika ISWAP Ta kashe Sama da mutane 120 a Borno.
Har Ila yau tace ko a Ranar 1- ga Satan Yuni yan Ta’addan sun kashe Limami da mai gari a Borno, sannan Ranar 9-ga watan Yuni an kashe wani Pasto da matarsa mai Juna Biyu a Taraba.
Sannan ga kisan da A kayi Na kwannan a Garin Kadisau ta Jahar Katsina Wanda yayi sanadiyar Kashe Sama da mutum Hamsin a Garin, Wanda hakan yayi sanadiyar Matasan Yankin Shiga zanga Zangar Lumana Na kin amincewa da Kisan da yan ta’adda keyi a Yankin Arewa.
A Shekaran Jiya mah Kungiyar dake Rajin Kare hakkin Dan Adam AMNESTY INTERNATIONAL Ta Ce Gwamnati Buhari Ta kasa Kare Rayukan Al’ummar ta.