Siyasa
Gwamnatin Bauchi Ta Cikawa ‘Yan Achaba Alkawarin Da Ya Yi Musu….

Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnan Jahar Bauchi Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi Ya cika alkawarin da ya dauka na Samarwa Yan Achaba da aka Hanasu Kabu kabu a wasu jahohi Domin Rage musu Radadin Talauci a lokacin zaman gida kan CoronaVirus.
Kauran Bauchi Tuni ya Kawo Mashinan masu Kafa Uku Rabawa kawai Ya rage Ayi.
Al’ummar Jahar sun nuna Farin cikinsu Matuka Ganin yadda Gwamnan ya cika Al’kawarin Cikin Lokaci.