Labarai

Gwamnatin Bauchi Tana Kashewa Kowanne Mutum Da Yake Dauke Da Cutar Covid – 19 Naira 1,500 Wajen Siyan Abinci — Mahukunta

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

Hukumar Lura Da Lafiya a Matakin Farko Ta Jihar Bauchi PHCDA, Ta Bayyana Cewar Gwamnatin Jihar Ta Bauchi tana Kashewa Kowanne Marar Lafiya Da yake Dauke da Cutar Sarkewar Numfashi Ta Covid – 19 kudi kimanin Naira 1,500 Wajen Sayan Abincin Da Marar Lafiya Zaici a Lokaci Guda.

Dr. Rilwanu Mohammed Wanda Shine Shugaban Hukumar a Jihar Ta Bauchi, Shi ya Bayyana Hakan a Jiya Lahadi, A Lokacin Zantawarsu Da Kamfanin Dillancin Labarai Na Kasa a Jihar Bauchi. Mohammed Wanda kuma Shine Shugaban Kwamitin Tuntuba Kan Wannan Annoba Ta Corona Virus a Jihar Ta Bauchi, Ya kara Da Cewar Gwamnan Jihar Bala Mohammad (Kauran Bauchi) ya Bada Umarnin Ciyarda Marasa Lafiyar Abincin Da Farashinsa Bai Gaza 1,500 dinbane A Kokarinsa Na Ganin Cewar An Ciyar Da Marasa Lafiyar Da Ingantacce kuma Tsabtataccen Abinci.

Sannan ya kara Da Cewar Hikimar Yin Hakan Kuwa Itace Domin a tabbatar Da Cewar Marasa Lafiyar Basu Gaza Samun Abincin Da ya haura Wanda Suke ci a Gidajensu ba, Tare kuma Da Rage musu Radadin Wannan Cuta da suke fama Da ita.

A Zantawarsu Ta Wayar Tarho Da Wasu Daga Cikin Al’umma, Shugaban Hukumar Ta PHCDA, ya Bayyana Cewar Ganin Kulawar Da Mutanen Da Suke Killace a Cibiyoyin Killacewar Jihar suke samune yasa har wasu daga Cikin Al’umma Wadanda ba Cutar ce take Damunsu bama suketa kira Da A killacesu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button