Siyasa

Gwamnatin Buhari Da Jami’anta Sunfi Tsoron Turawan Yamma Fiye Da Allah Da Ya Halicce Su, Inji Buba Galadima.

Spread the love

Tsohon Na Hannun Daman Shugaba Buhari Injiniya Buba Galadima Ya Ce Gwamnatin Buhari Da Jami’anta Sunfi Tsoron Turawan Yamma Akan Allah Da Ya Halicce Su, Kuma Suna Tsoron Turawan Don Kudin Da Suke Dasu A Kasashensu..

A zaben jihar Edo da ya gabata dai an bayyana cewa kasar Amurka da Ingila suna daga cikin wadanda suka taka gagarumar rawa wajen yin sahihin zabe mai inganci a jihar Edo kamar yadda daya daga cikin jiga-jigan jam’iyar adawa ta PDP Injiniya Buba Galadima ya fada, ya kara da cewa a sanarwar da kasashen suka fitar gabannin zaben inda suka ce zasu saka takunkumi ga ‘yan Najeriya masu magudin zabe tana daga cikin ababen da suka sa jam’iyya mai mulki ta APC ta fasa yin magudin zaben a cewar Buba Galadima.

Buba Galadiman dai har ila yau ya kara da cewa jami’an gwamnatin suna tsoron turawan ne don suna da kudade a kasashen na turai.

Daga Bappah Haruna Bajoga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button