Gwamnatin Buhari ta qi aminta da shawarata ~Atiku
Alhaji Atiku Abubakar, tsohon Mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar Peoples Democratic Party a zaben da ya gabata, ya bayar da babban dalilin sa Najeriya ta sake fadawa cikin wani mawuyacin hali.
Atiku ya ce dole ne wannan gwamnatin ta Shugaba Muhammadu Buhari ta hadiye girman ta, kuma ta amince da iyakokinta.
A cewarsa, gwamnatin mai ci ta ki bin shawararsa da ta sauran ‘yan kasa masu kyakkyawar ma’ana.
Atiku ya ce ya sami tabbacin sake faduwar tattalin arziki, a karo na biyu a cikin shekaru biyar, tare da damuwa.
Saboda ana iya kauce wa wannan idan da wannan gwamnatin ta kula da shawarwarin kishin kasa da ni da wasu ‘yan Najeriya suka bayar a kan rage kudin gudanar da mulki, da kauce wa karbar bashi, “in ji Atiku a wata sanarwa da ya raba a shafinsa na Twitter. a safiyar Lahadi.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya lura cewa duk da cutar ta COVID-19, ana iya kaucewa koma bayan tattalin arziki karo na biyu ta hanyar bin tsarin tattalin arziki.
Atiku, duk da haka, ya ce dole ne kowa ya mai da hankali kan mafita a wannan lokacin, ya kara da cewa Najeriya na bukatar shugabanci mai mahimmanci don jagorantar ta ga tafarkin dorewar tattalin arziki. Tsohon dan takarar shugaban kasar ya nuna cewa rashin mutuntaka ne ga gwamnati ta kara kudin kayayyaki da aiyuka wadanda suka shafi talakawa, tare da sanya tsadar kayan more rayuwa cikin daidaito.
Atiku ya gargadi gwamnatin Buhari game da ci gaba da karbar bashi
Ina kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta hadiye girmanta, kuma ta yarda da iyakokinta, ta yadda za su bude tunaninsu ga ra’ayoyin Jama’a ba tare da kula da girman Kai ba