Labarai
Gwamnatin Buhari tace Babu wani Batun Karin Farashin kudin wutar Lantarki.
Hukumar gudanarwar Kula da Wutar Lantarki a Najeriya, NERC, ta ce babu wani karin kashi 50 cikin 100 na harajin wutar lantarki.
Wannan ya bayyana ne ta bakin Shugaban Hulda da Jama’a na NERC, Micheal Faloseyi, a cikin wata sanarwa Daya fitar a Abuja ranar Talata.
Mista Faloseyi ya yi magana a kan yadda wasu wuraren suka ce an kara kudin wutar lantarki da kashi 50 cikin 100.
Ya ce: “Don haka ne hukumar ta bayyana ba tare da wata shakka ba cewa ba a ba da izinin amincewa da karin kashi 50 cikin 100 na kudin kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DISCOs, wanda ya fara aiki daga 1 ga Janairu, 2021. Ba
.