Uncategorized

Gwamnatin Buhari Tana Bin Talawa da Abinci Har Gidajensu~ Minista Isah Ali Pantami.

Spread the love

Ahmed T. Adam Bagas

Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Pantami ya bayyana cewa
Gwamnatin Buhari Tana Bin Talawa da Abinci Har Gidajen su.
Ministan ya bayyana hakan ne cikin wani Video na
tattaunawa da suke da wata baturiya.

Shehin Malam yace Wannan gwamnati ta ware kuɗaɗe masu
ɗumbin yawa don tallafawa talakawa a wannan yanayi na
zaman gida.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da aka bi don raba tallafin shine
amfani da rigistar layin waya don gane talaucin da mutane suke ciki.

Yanzu haka duk sati gwamnati tana raba wa da yawan yan
ƙasa abinci kai tsaye zuwa gidajen su don rage masu
raɗaɗin zaman gida.

Muna gane talakawan ta hanyar saka katin waya da suke yi,
wasu suna saka katin ƙasa da dala daya a wata ko dala 2 a
wata.

Ku Biyomu Zamu Kawo Muku Vedion Anjima.

Masu karatu Wannan Rabon Kayan Abincin Ko Yakawo Gareku???

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button