Gwamnatin Buhari Zata Siyar Da Matatun Mai Guda Hudu Da Kasarnan Take Dasu.
Gwamnatin Najeriya karkashin Mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tace zata saida Matatun mai guda hudu da kasarnan take tunkaho dasu.
Shugaban Kamfanin Man Fetur na kasa, Mele Kolo Kyari ne ya sanar da hakan a yayin wata hira da gidan Talbijin na Channel TV.
Kyari yace zasu sayarwa ‘yan kasuwa Matatun ya zama kudin kasa kadan ne zai rage cikin masa’antar.
Kyari yace Matatun zasu zama kamar yadda NLG take a yanzu Inji Shi.
Ya cigaba da cewa yanzu haka Ana Nan Ana cinikin Matatun, Sai dai bai bayyana sunan wanda zasu sayi Matatun ba.
Kyari ya bayyana Wannan Maganar duk da Kasarnan na cikin Rudani Kan Karin Kudin Man Fetur da Wutar Lantarki, Inda yanzu haka wasu kungiyoyi da ‘yan siyasa suka nuna Rashin amincewar su, akan Farashin Man.
Yanzu haka kungiyar kwadago ta NLC da UTC sun baiwa gwamnati Wa’adin Makonni 2 ko ta janye kudurinta na karin kudin Man ko Ayi zanga-zanga nuna adawa da karin kudin.
Idan baku mantaba, Shugaba Buhari yayi Ikirarin Zai gyara Dukkan Matatun Man Kasar Nan, Sannan Zai Kirkiri Sabbi a lokacin da yake Yakin Neman Zabensa na Shekara ta 2015, sai dai Yanzu ‘Yan Kasar Sun Kusa Ganin Sabanin Abinda Shugaban Ya fada kan Matatun Man Kasar.