Wasanni
Gwamnatin Jahar Kano ta Amince a Buda gidajen Kallon Kwallon Kafa (Ball).
Gwamnan Jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya Amince da bude gidajen Kwallon kafa dake Fadin Jahar bisa Ka’idojin da Hukumar Lafiya da gwamnati ta Gindaya musu.
Ganduje yayi wannan Jawabin ne lokacin shugaban masu gidan kallon Sharu Ahalan da tawagarsa suka Ziyarci gwamnan. Gwamnan ya gindaya musu sharruda kamar haka:- wanke Hannu, sa takunkumi, bada tazara. Sannan Gwamnan Ya basu Takunkumi domin Rabawa a gidan Kollon.
Daga Ahmed T. Adam Bagas