Rahotanni
Gwamnatin Jahar Legas Ta Sassauta Dokar Hana Zirga-Zirga Daga 9:00am Zuwa 3:00pm.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Gwamnan jahar ta legas ya baiyana sassauta dokar hana zirga zirga a fadin jahar, inda ya baiyana cewa gwamnati ta yarjewa gidajen abinci da kasuwanni ne kawai.
Gwamnan Babajide Sanwo-Olu shine ya baiyana hakan a yau laraba yayin dayake hira da gidajen talvision na jahar.
Cikin jawabin nasa ya baiyana cewa daga karfe 9:00am zuwa 3:00pm aka sahhalewa yan kasuwa da wuraren cin abincin kawai su bude a ranakun da aka Sanya musu na fita a jahar.
A karshe gwamnan ya sake jaddada cewa dukkan makarantu a fadin jahar suna nan a kulle kamar yadda gwamnati ta umarcesu tun bullowar cutar corona virus.