Labarai

Gwamnatin Jahar Legas Zata Samawa Al’ummar Jahar Data Kyauta Don Inganta Karatu A Yanar Gizo.

Spread the love

Gwamnatin Jahar Legas ta kudiri aniyar samarwa al’ummar Jahar kyautar Data don inganta harkar karatu a yanar gizo.

Gwamnan Jahar Legas Babajide Sanwo Olu shine ya bayyana hakan a gida Gwamnatin Jahar.

Sanwo Olu ya bayyana cewa zasu gudanarda taro tare da dukkan masu ruwa da tsaki a Jahar.

Olu yace sun yace sun bullo da wannan yunkurin ne a wani mataki na inganta fannin ilimi a wannan lokaci da ake fama da kwayar cutar Annobar Coronavirus dake addabar Jahar Legas, Najeriya, dama duniya baki daya.

Gwamnan yace zasu tattauna kan inganta Karin gudun yanar gizo a jahar.

“Bamuda wata Wasika da muka mikawa kamfanonin sadarwa a dai dai wannan lokaci, amma kamfanonin sun san cewa jahar Legas Babbar cibiyar kasuwancinsu ne”

“Watakila zamu bukaci shiga daki da kamfanonin sadarwar don tattaunawa wannan matsala” in Olu.

Yaci gaba da cewa ” Gwamnatin jahar Legas na kokarin cimma matsaya da masu ruwa da tsaki a fannin ilimin jahar”

“Akwai bukatar makarantu su maida hankali kan koyarwa a yanar gizo, a wannan lokaci da Ake fama da Dokar kulle ko zaman gida”

“Ina mai farincikin sanar daku cewa mun fara shirin koyarda daliban makarantu na gaba da sakandare, kuma zamu basu dukkan gudumuwa dakuma taimakon da ya dace”

“Muna Kara samun sabbin masu daukar darussa a yanar gizo daga Makarantun gwamnati, saboda haka muna Kira ga makarantu masu zaman kansu da suma suyi kokarin bullo da wannan shiri”

” zamuci gaba da wannan shiri har sai ranarda Gwamnatin tarayya zata bude makarantu” inji Gwamna Sanwo Olu na jahar Legas.

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button