Rahotanni
Gwamnatin Jahar Neja ta bada Aikin Titin Minna zuwa Bidda…………
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnatin Jahar Neja Ta bada aikin Hanyar da Ta Hada Minna Babban Birnin Jahar da Karamar Hukumar Bidda ta Jahar.
Aikin Wanda Gwamna Abubakar Sani Bello ya Baiwa Kamfanin (Dantata and Sowoe) Hanyar Mai Tsawon kilomita 82 da Zai lashe Kudi Naira Biliyan 23.9B.
Gwamnan ya yi Kira ga Kamfanin Da Su tabbatar sunyi aiki Mai Inganci sannan akan Lokaci, Aikin Wanda Tai Dauki Tsawon Watanni 18.
Gwamnan Yayi kira ga Mazauna Kauyuka da suke Kan Hanyar da Drebobi masu bin Hanyar da Su baiwa Masu Aikin Hanyar Hadin kai domin Atabbatar Anyi Aikin akan Lokaci.
Gwamnan ya kara da cewa Wannan Hanyar Nada Matukar Mahimmanci ga Al’ummar Jahar.