Gwamnatin Jahar Neja ta Kama Dan Jarida da Ya Fasa Kwai.
A daren Jiya Juma’a ne dai Yan Sanda suka Kama Wani Kwararren Dan Jarida Yahaya Usman a Gidansa dake Minna babban Birnin Jahar Neja.
Dan Jaridar an Kamashi ne Bayan Ya Rubuta Cewa Gwamnan Jahar Neja Abubakar Sani Bello, Ya ciyo Bashin Naira Biliyan Uku da miliyan Dari biyar a Bankin Zaneth alhali bai sanar da Al’ummar Jahar ba.
Usama wanda yace Gwamnan ya ciyo bashin ne ba Bisa ka’idaba Gwamna Bello ya ciyo bashin ne Cikin Watan afrilun wannan Shekarar.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnan Jahar ne ya Sa `Yan Sanda Su kama Dan Jaridar Inda yace Dan jaridar ya Tona Asirin Gwamnati, dalilin Haka Jami’an Tsaron Suka dira Gidan Usman sukayi Awun gaba dashi.
Sai dai Kungiyar Kare Hakkin Dimokuradiyya da Hakkin Dan Adam Tayi Kira da A Gaggauta Sakin Dan Jaridar, Inda kungiyar tace kama Shi Tauye hakkin Dan Adam ne, Kuma Katsa landan ne ga Aikin Jarida a Kasar Nan.
Wanda yayi kiran da muryan Kungiyar Mr. Deji Adeyanju ya Kira Usaman da Kwararren Dan Jarida ne Kwararre wanda Najeriya ke Alfari Dashi.
Deji yace kungiyar su Tayi Tir da Allah wadai Kan Kama dan Jaridar wanda Yan Sanda Suka Tsare shi Suna Azabtar Dashi a Hannun su Inji Shi.
Ahmed T. Adam Bagas