Lafiya

Gwamnatin Jahar Neja Ta Tsagaita Lokacin Zirga Zirga A Wasu Sassan Jahar.

Spread the love

Ahmed T. Adam Bagas

Gwamnan Jahar Neja Gwamna Abubakar Sadik Sani Bello LoLo Ya Ya ce Ya Takaita Lokacin Takaita Zirga Zigar ne Daga 8 Na Safe zuwa 2 Na yamma, Sa6anin 10 Na Safe zuwa 12 Na dare Da Ake yi A Baya.
Wannan Alfarmar Ta Gwamnan Ta farune Biyo bayan Fadi Tashi da Chiarman din Kasuwar A.A KURE ULTRAL MORDERN MARKET MINNA Alhaji. Yusus Muhammad Koshe Ya yi.

Koshe ya Nemi Alfarmar a Wajen Shugaban Karamar Hukumar Chancaga Hon. Abubakar Lalalo cewar Ya nema musu Alfarmar Abude musu Kasuwa Koda Na Awan ni Uku ne Domin Yan kasuwa su Sami Abinda zasu sa a Bakin Salati.
Kuma Hon. Lalalo yayi masa Wannan alfarma Nan Take Ya Nemi Alfarmar a Wajen Sakataren Gwamnatin Jahar Hon. Ibrahim Ahmad Matane Ya Sadasu da Gwamnan Kuma Gwamnan Yayiwa Bayanin su Kallon Tsanaki Sannan Ya Basu Tabbacin Daga Gobe Litinin 06-04-2020 A Bude Kasuwar Ga Yan Kasuwa Suci Kasuwa Daga 8 Na safe Har 2 Na yamma.

Sakataren Gwamnatin Jahar ne Ya yi wannan Jawabin A madadin Gwamnan Jahar.
Ahmad Matane yace An Dauki Dokakar Kulle Kasuwanin ne Da Takaita Zirga Zirga da Sauran Al’amuran Yau da Kullum a Jahar Dan Gudun Samuwar ko yaduwar Cutar nan Da ta addabi Duniya Wato Corona Virus.

Daga Karshe Chiarman din Kasuwar Chancaga Alhaji. Yusuf Muhammad Koshe ya Nuna Matukar Godiyarsa Ga Gwamnan Jahar Neja musamman ma Shugaban Karamar Hukumar Chancaga Inda Yace Shi ne Silar bude musu kasuwa Kuma Yayiwa Lalalo Addu’ar Samun Nasara Kan Shugabancisa da Addu’ar Wannan Cutar ta Covid-19 Allah ya Tsare Jaharsu Ta Neja Da Ita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button