Gwamnatin Jahar Neja Ta Tusa Keyar Almajirai 327 zuwa Garuruwansu.

Gwamnatin Jahar Karkashin Kwamishiniyar Ilmi ta Jahar Kuma Shugabar Kwamitin Yaki da Barace Baracen Almajirai a Jahar Hajiya Hannatu Jibrin Salihu ce Ta Tabbatar Da Hakan Ga Manema Labaru Jiya a Minna Babban Birnin Jahar.
Hannatu Tace An Sauki Wannan Matakin ne Yaddar Gwamnonin Arewa da Zummar Haramta Barace Barace a Yankin da Kuma Kokarin Hana Yaduwar Covid-19 Tsakanin Al’umma.
Hannatu Tace An Tara Al’majiran ne a Sansanin Mahajjata dake Tudun Fulani a Karamar Hukumar Bossa dake Kwaryar Minna, Sannan Aka musu Gwajin Corona aka Tabbatar da Ingancin Lafiyar su kana Aka Turasu Jahohinsu na Asali.
Almajiran dai Sun Fito ne daga Jahohin:-
Katsina 73
Kaduna 47
Kogi.
Kano. 15 sauran Sun hada da Zamfara, Kebbi, Abuja, Gombe, Sokoto, Taraba, Kwara, Oyo. Sai Kasar Ghana mutane 2.
Sai Dai Idan Baku manta ba Wasu Gwamnoni Sunce Bazasu Kori Al’majirai a Jahohinsu ba, Gwamnonin Sun Hada da:- Yobe, Borno, Zamfara, Sokoto da Sauransu.
Ahmed T. Adam Bagas