Gwamnatin Jahar Sokoto ta Karbi yan Asalin Jahar 17 da Sojoji suka Ceto a Zamfara.

Gwamnan Jahar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal Ya Karbi Wasu Mutane Yan Asalin Jahar da Masu Garkuwa da mutane Suka Sace zuwa Makobtar Jahar.
Tambuwal Din ya Nuna matukar Farin Cikinsa ga wakilan Gwamnan Zamfara Sannan ya Jinjinawa Sojojin Bisa Namijin Kokarin da Sukayi Yadda Suka Ceto Muten 17 Cikin Koshin Lafiya.
Tambuwal yayi kira ga Al’ummar Jahar Sokoto da Surika Taimakawa jami’an Tsaro da Bayanan Sirri domin Kawarda Aiyukan Yan Ta’adda a Jahar dama Kasa Baki Daya.
Kwamishinan Kula da Harkokin Tsaro da Ma’aikatan Tsaro Na Jahar Sokoto Ritaya. Kanar Garba Moyi yace Mutane Da Aka Ceto 16 daga cikinsu yan Karamar Hukumar Tureta ne, 1 kuma Dan Karamar Hukumar Rabah ne duk a Jahar Sokoto.
Allah ya Shiga Tsakanin Na Gari da Mugu!.
Daga Ahmed T. Adam Bagas