Kasuwanci

Gwamnatin Jihar Adamawa Ta Sasanta Rikicin ‘Yan Kungiyar Keke-Napep Dake Garin Numan, Har Sun Cigaba Da Gudanar Da Sana’arsu A Yau, Kamar Yadda Suka Saba Don Dogaro Dakai, Bayan Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Mika Kokensu Cikin Kasa Da Sa’o’i 40

Spread the love

ALHAMDULILLAH

…Masu sana’ar Keke-Napep dake garin Numan, sun mika godiyansu, tare da yiwa kungiyar “Arewa Media Writers” ruwan Addu’o’i, kan namijin kokarin da take yi wajan ganin ta kawo wa al’ummar yankin Arewa cigaba mai daurewa.

Daga Kungiyar “Arewa Media Writers”

Gwamnatin Jihar Adamawa ta sasanta rikicin ‘yan kungiyar Keke-Napep dake garin Numan, har sun cigaba da gudanar da sana’arsu a yau, kamar yadda suka saba gudanar wa don dogaro dakai, bayan kungiyar “Arewa Media Writers” ta mika kokensu cikin kasa da sa’o’i 40.

Idan masu karatu basu manta ba, a jiya Alhamis da Safe kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” ta wallafa kokensu cikin gaggawa akan matsalar rikicin Shugabancin kungiyar ‘yan Keke-Napep da ya kunno kai a garin wanda hakan ya sabbaba gwamnatin jihar ta dakatar da aikin masu adaidaita sahun a dukkannin fadin garin.

Hakan yasa dubunnan al’umma da suka dogara da sana’ar suka zama masu zaman kashe Wando, bayan dawainiyar iyalai, ‘yaya, iyaye, ‘yan uwa dake kansu.

Zuwa yanzu farin ciki ya dumulmule illahirin dukkannin masu sana’ar Keke-Napep suna ta jinjinawa kungiyar “Arewa Media Writers” tare da yiwa kungiyar addu’ar fatan Alkhairi, ga dukkannin Mambobin kungiyar na kasa baki daya, da suka bada gudummuwarsu wajan isar musu da sakon su ga gwamnatin jihar har ta karbi koken su.

Haka zalika kungiyar “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, da shugaban kungiyar reshen jihar Adamawa Muhammad Bashir Yola, take jinjinawa gwamnatin jihar Adamawa kan namijin kokarin da tayi wajan karbar koken al’ummar garin.

Wannan kadan daga cikin burin kungiyar “Arewa Media Writers” kennan, don ganin ta farantawa dukkannin illahirin al’ummar yankin Arewa.

Kungiyar “Arewa Media Writers” tana bukatar Addu’o’i daga gareku Allah ya shige mata gaba kan muhimman ayyukan da ta saka a gaba, don kawo wa yankin Arewa cigaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button