Ilimi

Gwamnatin Jihar Jigawa Zata Saka Almajirai 1,322 Da Aka Dawo Mata Dasu A Makarantun Gwamnati.

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda.

Gwamnatin Jihar ta Jigawa ta Bayyana cewar Zata Saka Almajirai 1,322 da Aka Dawo Mata Dasu Daga Mabanbantan Jihohin Kasarnan a Makarantun Gwamnatin Jihar.

Gwamnan Jihar ta Jigawa Muhamad Badaru Abubakar ne ya Bayyana Hakan a Babban Birnin Jihar na Dutse, Lokacin da yake Ganawa da Manema Labarai kan Matakan da Gwamnatin Jihar ta Jigawa take Dauka a Kokarinta na Dakile Yaduwar Annobar Cutar Covid – 19 a Fadin Jihar.

Inda Muka Jiyo Gwamnan yana Cewa “Kamar Yadda na fada a Tattaunawarmu Data Gabata, Kimanin Almajirai 1,345 ne Aka Dawo Mana Dasu Daga Mabanbantan Jihohin Kasarnan. Mun Lura Dasu Tareda Basu Kulawa, Haka Zalika mun Samar musu da Abubuwan More Rayuwa, Bugu da Kari Kuma Mun Lura da Lafiyarsu.

“Dukkannin wadannan Almajirai mun Dankasu a Hannun Iyayensu, In banda 23 daga cikinsu, wadanda sakamakon Gwajinsu yanuna cewar Suna Dauke da Ciwon Covid – 19, Wanda a yanzu haka an killacesu, kuma Ana Cigaba da Basu Magunguna”.

” Saboda haka Zamu Saka Wadannan Almajirai da Aka tabbatar da Koshin Lafiyarsu a Makarantun Firamare na Gwamnati Domin Samun Ilimin Zamani, Haka Zalika zasuci Gaba da karatunsu na Alqur’ani Maigirma ” A Cewar Gwamnan Jigawa Muhamad Badaru.

Haka Zalika Gwamnan yakara da Cewar Ana Samun Cigaba a Yakin da Gwamnatin Jihar takeyi da Annobar Covid – 19, Duba da Yadda Ake Samun Raguwar Masu Kamuwa Da Cutar a Jihar ta Jigawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button