Rahotanni

Gwamnatin jihar Kaduna ta bi dare har gidan nakasassu da ke Kano road ta yi awan gaba da su, har zuwa yanzu ba a san inda suke ba.

Spread the love

Shugaban nakasassu Na jihar Kaduna ya ce gwamnati ta yaudare su gabannin zaben 2019, an nuna za a yi da su, harma aka ce musu su nemi wani waje su taru a can duk Wanda yayi niyyar taimakon su to ya bisu can, yace duk sun cika umarnin gwamnati, yanzu kuma an Afko musu cikin dare duk an kame su.

Ya ce “gwamna El-rufa’i ya sani su ba su ne suka halicci kansu a haka ba, Allah ne yaso ya gansu haka.”

Ya kara da cewa “akwai wadanda saboda nakasar su ko sana’a ba za su iya yi ba, to irin wadannan ka hanasu bara kace su taru a wani waje, sun taru a can din kuma kabisu can din ma duk ka kame su, yanzu Yaya gwamna yake so suyi?”

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button