Gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da malaman firamare 1,288 da aka kora daga aiki a watan Yunin 2022 bayan kammala jarrabawar tantancewa
Malamai 1,266 da aka dawo da su aikinsu ne jarabawar cancantar ta shafa, yayin da aka cire wasu 22 daga cikin albashin gwamnati bisa zarginsu da ba a tabbatar da su ba.
Gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da malaman firamare 1,288 da aka kora daga aiki a watan Yunin 2022 bayan kammala jarrabawar tantancewa.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ta hannun kakakin hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar, Misis Hauwa Mohammed.
Sanarwar ta bayyana cewa, malaman da aka dawo da su 1,266 jarabawar cancantar ta shafe su, yayin da wasu 22 kuma aka cire su daga cikin albashin gwamnati bisa zargin da ake musu na rashin gaskiya.
Hukumar ta bayyana cewa an kori malamai 1,288 daga cikin 2,192 saboda rashin cin jarabawar da suka yi, yayin da wasu 165 aka kore su saboda rashin aikin yi.
Sai dai bayan nazari tare da tantance korafe-korafen da malaman da abin ya shafa suka gabatar ciki har da wadanda aka kora bisa kuskure bayan cin jarabawar da kuma wadanda ba su da lafiya a lokacin da aka gudanar da aikin, gwamnatin jihar Kaduna ta amince da mayar da malamai 392 da suka yi rubuce-rubuce da kuma sun ci jarabawar cancanta da wasu ma’aikatan gwamnatin tsakiya 515 wadanda a hukumance aka cire su daga jarabawar.
Sauran wadanda aka dawo da su aiki sun hada da malamai 298 da aka tabbatar da cewa ba su da lafiya a lokacin jarabawar, da kuma malamai 61 da aka yi garkuwa da su ko kuma suka yi hatsari da Sakatarorin Ilimin nasu suka tabbatar. Haka kuma, an mayar da malamai 22, wadanda aka cire na dindindin daga cikin albashin ma’aikata saboda wasu da’awar da ba a tabbatar da su ba, wadanda adadinsu ya kai 1,288 da aka mayar da su bakin aikinsu.
Don haka Hukumar ta shawarci dukkan malaman da abin ya shafa da su tattara wasikun mayar da su daga Sakatarorin Ilimin nasu cikin gaggawa.