Labarai

Gwamnatin jihar Kaduna ta nemi kasar Saudiyya ta saka hannun jari da tallafi a jihar.

Spread the love

Mataimakiyar gwamna Dr Hadiza Sabuwa Balarabe ta bayyana hakan a wani taron murnar cikar masarautar Saudiyya karo na 93 a cibiyar taron The Afficent, da akayi a Kano ranar Asabar.

A nata jawabin, mataimakiyar gwamnan ta godewa Masarautar Saudiyya bisa wannan kyakkyawar niyya da kuma ci gaba da tallafawa Najeriya da jihar Kano da kuma Kaduna.

Ta ci gaba da cewa kofar jihar Kaduna a bude take domin kasuwanci, ta kuma bukaci a kara ba da tallafi daga Kindom of Saudi zuwa jihar Kaduna musamman a fannin zuba jari.

Ta ce, “Na tsaya a nan ina wakiltar Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani wanda Bai samun hakartar wanna taron ba Ya bukace ni da in mika sakon gaisuwarsa ga karamin jakadanci da al’ummar masarautar Saudiyya.

“Ina so in gode muku kan duk goyon bayan da kuke ba Najeriya, Kano da kuma jihar Kaduna. Muna addu’ar Allah ya kara mana albarka.

Jihar Kaduna ta dade tana bude harkokin kasuwanci. Mun fadada iyakokinmu kuma muna fatan za mu ji tasirin zaman ku a jihar Kaduna domin zai iya bude bangarori da dama don hadin gwiwa a fannonin ilimi, lafiya da sauransu.

Muna mai da hankali kan bunkasa jarin dan Adam kuma muna fatan kokarin da muke yi a wannan fanni ya sami karin tallafin da za mu samu daga Masarautar Saudiyya.

“A madadin jama’a da gwamnatin jihar Kaduna, ina cewa muna taya mu murna, muna kuma addu’ar Allah ya bamu albarkar ranar kasa baki daya.”

Taron ya samu halartar babban jakadan masarautar Saudiyya, mai girma Khalil Ahmed Alwami, ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda ya kasance babban bako. Gwamnonin jihohin Kaduna, Jigawa, Gombe da Zamfara sun samu wakilcin mataimakansu.

Sauran manyan baki sun hada da Sarkin Kano da Sarkin Musulmi da dukkansu da jami’an gwamnati da shugabannin masana’antu da jami’an difloma da sauran manyan mutane.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button