Labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Tsawaita Dokar Kullen Zaman Gida Da Karin Makonni Biyu

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

Biyo Bayan Karewar Wa’adin Wata Guda Ta Dokar Kullen Zaman Gida Da Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kakaba, a Jiya Talata Ma Gwamnatin Jihar Ta Bayyana Karin Makonni Biyu a Wa’adin Dokar Ta Zaman Gida a Fadin Jihar Ta Kaduna a Kokarin Ta Na Ganin Ta Shawo Kan Annobar COVID – 19 Da Aka Samu Barkewarta a Jihar.

Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ce Ta Sanar Da Hakan a Jiya Talata, Lokacin Da take yiwa Al’ummar Jihar Jawabi a Kafafen Yada Labaran Jihar.

Saidai kuma Lamarin Bai yiwa Mafi Yawan Al’ummar Jihar Dadi ba, Inda har wasu Daga Cikinsu ma Suke Bayyana Cewar Basuyi Tsammanin Gwamnatin Kadunan Zata Tsawaita Wa’adin Dokar Kullen Zaman Gidan ba, A Yayinda a Daya Bangaren kuwa Wasu Daga Cikin Al’ummar Ke Bayyana Cewar Ai Daman Sun San Za’a Rina.

Fatanmu Dai Shine Allah yakawo Mana Karshen Wannan Annoba ta COVID – 19 Cikin Gaggawa Domin Dai Lamura Su Cigaba Da Wakana Yadda Suke a Baya, Ba tare Da An Cigaba Da Garkamemu a Gidajenmu Tare da Hanamu Fita Gurin Sana’o’inmu, Karatunmu Da Sauran Muhimman Abubuwan Da Suka Jibanci Rayuwar Dan Adam ba.

Dafatan Makarancin Wannan Labari Yayi Sallah Lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button