Labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Yi Shelar Hutu Ga Jama’a Don Juyayin Mutuwar Sarkin Zazzau.

Spread the love

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana Laraba, 23 ga Satumba, 2020 a matsayin ranar hutu don juyayin marigayi Sarkin Zazzau,) Alh. (Dr.) Shehu Idris.

Wannan ya kasance ne kamar yadda gwamnatin Kaduna ta sanar da makokin kwanaki uku na marigayi sarki wanda zai fara daga Litinin 21 ga Satumba zuwa Laraba 23rd Sept.

Sarkin ya kwashe shekaru 45 a kan karagar mulki bayan da ya hau gadon sarauta a shekarar 1975 yana da shekara 36.

A cikin wata sanarwa da aka gabatar a yau Litinin, dauke da sa hannun mai magana da yawun Gwamnan Muyiwa Adekeye, ya ce, “mazauna za su yi amfani da shi wannan lokacin don yin addua ga marigayin. ”

“Ofisoshin gwamnati za su bude kamar yadda aka saba kuma ana sa ran ayyukan na yau da gobe za su ci gaba a ranakun Litinin da Talata, yayin da za a yi hutu a ranar Laraba domin girmama shi da kuma gudanar da addu’o’i.

Sanarwar ta kara da cewa: “Tutoci za su tashi sama-sama daga Litinin, 21 ga Satumba zuwa Laraba, 23 ga Satumba 2020.”

Rahotanni sun nuna cewa sarki Idris ya mutu ne a wani asibitin sojoji da ke Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.

Tuni aka yi jana’izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button