Gwamnatin Jihar Kano Ta Karyata Jita-jitar Da Ake Yadawa Cewa Covid-19 Ce Ke Sanadiyyar Mutuwar Mutane A Jihar Kano

Spread the love

Daga Kabiru Ado Muhd.

Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar ganduje yace ba gaskiya bane zancen da wasu suke yadawa cewa kaso 43.3 daga cikin 100 Na wadanda suka rasa rayukansu a jihar kano Na daya daga cikin alamomin zazzabin covid-19, yace wannan zance ba gaskiya bane jita jitace kawai irin ta matasan kafafen sada zumunta.

Gwaman jihar kano Abdullahi Umar ganduje yace tabbas an gudanar da bincike kan yawan mace macen domin daukar kwararan matakai amma yadda sakamakon binciken ya nuna angano cewa yawan mace macen Nada alaka ne da ciwon hawan jini da ciwon sugar da kuma yanayin zafi da ake fama dashi da kuma sauran laurarai da ba a rasa Dan Adam dasu, amma kwata kwata yawan mace macen bashi da alaka da cutar covid-19 kamar yadda masu son tada zaune tsaye ke yadawa.

Gwamnan yace yana kira gamasu yada wannan jita jitar da suguji yada zantuttukan da ka iya daga hankulan jama a musamman a cikin irin wannan yanayi da al umma ke ciki.

Har ila yau gwamnan yayi kira ga al umma musamman al ummar jihar kano da suyi watsi da wannan labaran karyar ba gaskiya bane jita jita CE dabata asali bata da tushe.

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *