Siyasa

Gwamnatin Jihar Kano Ta Zabtare Albashin Masu Rike Da Mukaman Siyasa Da Kashi 50.

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya Bayyana Cewar Daga Yanzu Masu Rike Da Mukaman Siyasa a Jihar Kano za’a Dawo Biyansu Rabin Albashin Sune, Ma’ana Za’a Dawo Biyansu Kaso 50 Na Albashinsu Maimakon Cikakken Albashin da Aka Saba Biyansu A Kowanne Wata,

Inda Gwamnan ya Bayyana Cewar An dauki Wannan matakine Sakamakon Rashin Samun Isashshen Kudi daga Gwamnatin Tarayya dakuma Hukumar Tattara kudaden Shiga Ta Jihar Kano, Sakamakon Illar Da Cutar Covid – 19 Ta Haifar ga Tattalin Arziki,

A sanarwar Da Mai Magana Da yawun Gwamnan Jihar Kanon, Abba Anwar, ya fitar ya Bayyana Cewar Za'a fara Aiwatar Da Tsarinne daga Wannan Watan damuke Ciki Na Mayu.

Gwamnan ya Kara dacewa Gwamnatin Jihar Kano Ta Dauki Matakin Ragewa Masu Rike Da Ofisoshin Gwamnati Albashin ne Saboda Rashin Kudi Da Gwamnatin take Fama dashi, Sakamakon Faduwar Farashin Danyen Mai, wanda hakan yayiwa tattalin Arzikin Kasarnan Illa Matuka, Saboda Haka Babu Mafitar Da tawuce Rage Albashin,

Sannan yakara Dacewar Wadanda Rage Albashin ya shafa Sun hadarda Gwamna Da Mataimakinsa, Dukkannin Kwamishinoni, Masu bada Shawara, Mataimaka Na Musamman Da sauran Makamantansu,

A Matakin Karamar Hukuma kuwa Wadanda Abin Zai Shafa Sune Chairman, Da Mataimakinsa, Zababbun Kansiloli, Kansilolin Nadi, Masu Bada Shawara, dakuma Sakatarorin Kananan Hukumomi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button