Gwamnatin jihar Kano ta zaftare Albashin Ma’aikata a jihar na watan daya gabata.
Ma’aikata a jihar Kano sun koka kan yadda gwamnatin jiha ta zabtare musu kudade masu yawa a albashin su na watan Nuwambar da ta gabata.
Majiyarmu ta jaridar Kano Focus da wasu ma’aikata a jihar Kano sun bayyana yadda aka zabtare musu kudaden ba tare da sanin daliliba.
Wata Malama a hukumar kula da makaratun sakandire ta ce an zaftare mata har Naira 10,000 cikin albashin nata.
Ta ce ko kadan basu san dalilin cirar kudaden ba kuma ba a yi musu wani bayani na cewar za a cire musu ba.
Shi ma wani ma’aikacin yada labarai a nan Kano da aka yiwa yankan ya nuna takaicin sa kan irin halin rashin tausayin da aka nuna musu.
“Ni sun ciremin dubu 11,000 ma’aikatan da ke karkashin gwamnatin jihar Kano da kananan hukumomi an cire musu karin mafi karancin albashi ne.
To sai dai duk kokarin mu na jin ta bakin shugabar ma’akata ta jihar Kano Binta Lawan Ahmad al’amarin ya ci tura.