Labarai

Gwamnatin Jihar Kano za ta samar da gidaje ga Al’umma a wani Fili Hekta Ashirin da biyu.

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin hada gwiwa da duk wata kungiya da za ta taimaka wajen cimma burinta na samar da gidaje.

Manajan Daraktan Kamfanin Gidaje na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Rabi’u ne ya bayyana hakan a wani taro da mahukuntan kamfanin nan na Questcom Limited.

Alhaji Abdullahi Rabi’u ya bayyana cewa gwamnati mai ci a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ba da fifiko sosai wajen samar da matsuguni ga al’umma. Ya kara da cewa, shirye-shirye sun kai ga gina gidaje masu saukin kudi a kauyen Madinawa da ke karamar hukumar Kumbotso, inda tuni aka samar da fili kimanin hekta 22 domin aikin.

Da yake tsokaci jim kadan bayan kallon gabatarwar da shugaban kungiyar Questcom Limited ya gabatar, MD ya nuna godiya ga gaskiya da kuma kwarin gwiwar da kamfanin ke da shi na hada hannu da Kamfanin don bunkasa gidaje a jihar.

Alhaji Abdullahi Rabi’u, wanda ya dage kan samar da gidaje masu inganci da rahusa, ya bukaci kamfanin da ya fito domin kara tattaunawa kan yadda Kano za ta zama jaha kan gaba wajen bunkasa gidaje a fadin kasar nan. Daga nan sai ya yabawa kamfanin bisa nuna sha’awar yin hadin gwiwa da gwamnatin jihar ta hanyar kamfanin tare da ba su tabbacin bayar da hadin kai sosai wajen cimma manufofin da ake bukata.

Tun da farko, a jawabinsa, shugaban tawagar kamfanin, Architect Yeshua Russel, ya shaida wa manajan daraktan cewa, sun je harabar kamfanin ne domin gabatar da na’ura mai kwakwalwa kan yadda kamfanin ke gudanar da ayyukansa da kuma yiwuwar hada gwiwa da gwamnatin jihar.

Mista Yeshua ya lissafta nasarori da dama da kamfanin ya samu tare da danganta hakan ga himma da amfani da fasahar zamani.

Shugaban tawagar, Mista Yeshua, ya ce, kamfanin a ko da yaushe yana tabbatar da cika ka’idojin duniya, ya kuma bayyana fatan cewa, hadin gwiwarsu da kamfanin zai taimaka matuka wajen magance karancin gidaje, tare da cimma nasarar da aka dora masa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button