Labarai

Gwamnatin jihar kano Zata Bude manyan Makarantun Jami’o’i A Ranar 26 ga watan Octoba.

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta tsayar da ranar 26 ga watan Oktoba domin sake bude jami’oi’in mallakin jihar da sauran manyan makarantu don ci gaba da karatuttukan ilimi na 2019/2020.

Kwamishinar Ilimi mai zurfi ta jihar, Mariya Mahmoud, ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kano ranar Litinin.

Ta ce an cimma matsayar sake bude cibiyoyin ne a wata ganawa da ta yi da masu ruwa da tsaki, ta kara da cewa gwamnati ta lalata makarantun.

Ms Mahmoud ta ce gwamnati za ta samar da kayan kariya na sirri (PPE) ga dukkan cibiyoyin don kare daliban da kuma duba yaduwar kwayar cutar corona.

Makarantun firamare da sakandare a jihar sun ci gaba a ranar 12 ga watan Oktoba Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button